Shin Menene Alakar Rahama Sadau Da Rosey Meurer, Rosey Meurer Yan Asalin Addinin Christanchi Fitacciyar Yan Wasan Kudanchi, Abokiya Ko Kuma Nace Kawa Ga Rahama Sadau.
Kamar Yadda Kuka Sani Rahama Sadau Tafara Daukan Wasu Dabi'u Na Wata Abokiyarta Wanda Akafi Sani Da Rosey Meurer Domin Kuwa A Wani Dogon Bincike da Mukayi Akan Jarumar, Mun Gano Abubuwa Sosai Wanda Takeyi Dasuka Sabawa Addinin Musulunchi Da Kuma Al'adar Hausa Fulani.
Domin Kuwa Idan Baku Manta Ba Jaruma Rahama Sadau Takasance Tana Janyowa Kanta Abubuwan Magana iri - iri Daban-daban Domin Kuwa Tun A Shekarun Baya Dasuka Wuce Kamar Shekara Ta Dubu Biyu Da Sha Shida 2016 Jarumar Tafarayin Abubuwan Janyowa Kai Magana Masu Yawa.
Domin Kuwa A Wannan Shekara Ta 2016 Ne mukaga Tayi Wani Bidiyon Waka Da Fitaccen Mawakin Hausa Hip - hop Wato Buba Barnabas Wadda Akafi Sani Da (classiq) Acikin Bidiyon Wakar Munga Jarumar Ta Rungumeshi Wanda Itace Jarumar Data Tabayin Wani Abu Na Fasikanchi Wanda Ba'a Taba Samun Irin Haka Ba A Masana'antar ta Kannywood.
A Lokacin Da Wannan Abu Yafaru Sai Hukumar Tace Fina-finai Da Al'umma Sukayi Amata Raddi Kala-kala Da Tsinuwa Sai Muka Ga Jarumar Tayi Hijra Daga Nigeria Ta Koma Kasar Amurka Ta Zama Na Wasu Yan Lokuta, Har muka Ga Ta Wallafa Wani Sabon Hotonta A Shafinta Na Sada Zumunta Da Fitaccen Mawakin Kasar Amurka Wato Akon, Bayana Dawowar Jarumar Kasar Nigeria Munga Bata Tsaya Nanba Sai Ma Taci Gaba Da Janyowa Kai Abubuwan Magana Iri Daban -Daban.
Domin Kuwa A Shekara Ta 2019 Ne Mukaga Jarumar Ta Yi Wani Bikin Bude Sabon Gidan Abinchinta Mai Suna Sadau Home A Wannan Bude Gidan Abinchi Munga Jarumar Tayi Wasu Shigar Wani Kaya Wanda yajanyo Mata Zagi Da Tsinuwa Domin Kuwa Bisa la'akari Na Dubawa Bai Dace Kamarta Yar Hausa Fulani Kuma Musulma Ta Aikata Wannan Abunba.
Baya Da Haka A Shekarar Data Wuce ne Wato 2020 Jarumar Tasake Wani Abu Wanda Yayi Mata Silar Korarta Daga Kungiyar Kannywood A Karo Na Uku, Abunda Jarumar Tayi Bakomai Bane Face Wasu Kaya Data Saka Wanda ta Sanadiyyar Wannan Kaya Wani Yayi Batanchi Ga Annabi Muhammad (S A W) Wannna Dalilin Ne Mutane Da Dama Sukayi Ta Zaginta Daga Baya Jarumar Ta Goge Hoton Sannan Ta Bawa Mutane Hakuri Akan Haka.
Daga Karshe Hukumar Tace Fina-finai Ta Kori Jarumar Daga Masana'antar Kannywood Din Akan Wadannan Abubuwan Datakeyi Wanda Suke Janyowa Jaruman Masana'antar Zagi Da Kuma Tsinuwa A idon Al'ummah, To Daman Batun Yanzu Ba Jarumar Ta koma Harkar Fina-finan Kudunchin Kasar Nan Domin Tun a kOra Ta Farko Da Akayi Mata Ta Koma Harkar Fina-finan Kudanchin Kasar Nan.
To Sai Da Aka Koreta A Kashi Na Uku Sai Ta Koma Gadan Gadan Harkar Fina-finan Kudanchi , To Ba'a Nan Gizo Yake Saka Ba Domin Kuwa Jarumar Tagamu Da Wasu Abokan Aiki Wadanda Sukayi Tasiri Akanta Sosai Domin Kuwa Kamar Wannan Babbar Abokiyarv Tata Wadda Akafi Sani Da Rosy Meurer, Jaruma Rahama Sadau Tana Daukan Dabiunta Domin Irin Hotunan Da Jaruma Rosy Meurer Take Sakawa To Shi Rahama Sadau Take Sakawa.
Wannan Shine Ya Janyo Hankalina Akan Jarumar Domin Kuwa Ba Ficewarki Daga Masana'antar Ta Kannywood Shine Zai Baki Dama Ki Ci Gaba Da Abunda Kika Ga Dama Ba Domin Kuwa Har Yanzu Ke Musulma Ce Kuma musulmi Ako Ina Yake Yakamata Ya Rike Addininsa Dakuma Darajarsa Musamman Ma Idan Kikayi La'akari Da Kabilar Dakika Fito Hausa/fulani Yakamata Ki Nutsu Dan Allah Ko Kuma Nace Ki Chanha Salo Akan Abunda Kikeyi Rahama sadau.
Toh wannan Itace Shawarar Da Muke Baki Rahama Sadau Munaso Kuyi Share Din Videon Nan Domin Yaje Kunnen Rahama Sadau Domin Ta Chanja Salo Akan Abunda Takeyi Mungode.