Sunday, March 28, 2021

Bincike Ya Nuna Yanzu Tauraruwar Hamisu Breaker Ce Take Dagawa A Arewacin Nigeria

SHARE

 


A Wani Dogon Bincike Da Masana Sukayi A Bagaren Wakar Hausa Musamman Ta Yan Nanaye Ko Ince Masu Wakar Soyayyar Zamani.


A Iya Bincike Da Akayi Tauraruwar Hamisu Breaker Ita Ce Take Dagawa Sosai Bisa Ga Sauran Mawaka A Wannan Fanni Na Wakar Soyayya Acikin Masana'antar Kannywood, Idan Baku Mantaba A shekarun Dasuka Wuce Anyi Mawaka Masu Tarin Yawa A Arewachin Nigeria Wanda Mafiya Yawanchinsu Sun Fito Ne Acikin Masana'antar Kannywood.


Wadda A Shekarun Bayane Daga Shekara Ta 2014 Zuwa Shekara Ta 2018 Tauraruwar Wadannan Jaruman Wato Nura M Inuwa da Umar M Shareef Ta Haska Sosai Yadda Suka Samu Masoya Ta Kuma Tarin Mabiya Shafukan Sada Zumunta, Mawakan Guda Biyu Dai Sun Kasance Suna Waka Kusan Iri Daya Domin Kuwa Kowanne Yakan Iya Taka Rawar Gani A Fannin Wakar Abokin Gwaminsa.


Ma'ana Shi Umar M Shareef Yafi Yin Wakoki Dasuka Danganchi Soyayya Da Kuma Al'amuran Yau Da Kullum Baya Da Haka Shi Kuma Nura M Inuwa Ya Ta'allaka Ne A Bangaren Wakar Barkwanchi Da Kuma Soyayya Awani Fannin Duba Da Yadda Muka Ga Mawakan Guda Biyu Sukanyi Wakoki Biyu A Yawanchin Fina-finan Da Ake A Cikin Masana'antar Domin Kuwa A Ka'idar Film Din Hausa Anayin Waka Guda Biyu Ne Ta Tsakiyar Shiri Da Kuma Ta Karshen Shirin.


To Wadannan Mawakan sun Kasance Suna Aiwatar Da Aikin Wakokinsu Ne A Lokaci Guda Ma'ana Idan Aka Yi Film Akan Bukaci Umar M Shareef Yayi Waka Data Danganchi Soyayya Acikin Wannan Film Din Shikuma Nura M Inuwa Ana Bashi Bangaren Daya Dace Ba'a Fiya Bashi Wakokin Soyayya Sosai Acikin Film ba Sai Dai Wakar Sarauta Ko Kuna Ta wani Bangare Na Cin Nasara Acikin Film.


Kamar yadda Kuka Sani Zamani Ba Karya Bane Kuma Komai Tsawon Dare To Mun Tabbata Gari Zai Waye!!! Tun Daga Lokacin Da Wadannan Jarumai Kuma Mawaka Suka Taso Da Harkarsu Ta Waka Ba'a Samu Wani Mawaki Daya Sha Gabansu Ba Domin Mai Laya Ya Kiyayi Mai Zamani, Amma Kamar Yadda Mukayi Muku Bayani Akan Cewa Lokaci Ba Karya Bane Shine.


Bayan Bullowar Mawaki Hamisu Breaker Da Ado Gwanja Tunda Shi Ado Gwanja Bazamuyi Bayani Akansa Ba Domin Ba Wannan Bangaren Muka Dauko Ba , Shi Hamisu Breaker Lokacin Bayyanar Tauraruwarsa Domin ita Harkar Waka Wani Lokaci Tana Da Wani Irin Alhini, Ma'ana Sai Kaga Kana Tayin Wakoki Amma Baka Samu Karbuwa Daga Wajen Mutane Ba, Amma Idan Daukaka Ta Allah Tazo Sai Kuma Kaga Tauraruwarka Ta Haska Kafi Kowa.


To Bazamu Ce Ga Lokacin Da Hamisu Breaker Yafara Harkar Waka ba Amma Sai Dai Muce Ga Lokacin Da Tauraruwarsa Ta Haska, Hamisu Breaker Yayi Fitar Burgune Tun A Shekara Ta 2019 Lokacin Dayayi Wata Wakarsa Mai Suna Sirrin So, Wannan Wakar Tasamu Masoya Sosai A arewacin Nigeria Harma Da Wani Bangare Na Kudanchi.


Baya Da Haka Jarumin Bai Tsaya Anan Ba Yayi Wakoki Masu Yawa Kamar Wata Sabuwar Waka Dayayi Wanda Akalla Wakar Nan Da Hamisu Breaker Yayi Ta Samu Maziyarta Ko Masoya A Kalla Mutum million Goma A Shafin Youtube Da Sauran Kafofin Sada Zumunta, Wakar Jaruma Ta Hamisu Breaker Tayi Yawo Sosai A Lungu Da Sako Na Fadin Kasar Nigeria Harma Da Kasashen Ketare Cameroon Da Chad, Baya Da Haka Itace Ta Dago Da Martabar Mawakin Takaishi Inda Baiyi Zaton Yaje Ba.


Sannan Tasanadiyyar Wannan Wakar Jarumar Yarinyar Data Fito A Cikin Wakar Wato Mome Gombe Itama Tasamu Daukaka Tasanadiyyar Wannan Wakar, To Dama Haka Daukaka Take idan Allah Yaso Kasamu Daukaka A Lokaci Guda Zaka Sanu Kuma Duniya Tasanka kuma Kasamu Masoya Sosai, Baya Da Haka Mawaki Hamisu Breaker Yanayin Wakokine Salo Biyu Kamar Haka.


(1) Wakar Gidan Biki.

(2) Wakar Soyayya.


Idan A Halin Yanzu Mawaki Yarike Wannan Salo Guda Biyu Na Waka Toh Idan Daukaka Ta Sameshi Zai Yi Mamaki Domin Babu Abunda Yake Tashe Sama Da Harkar Gidan Biki Ma'ana Bangaren Aure, Kaga Kuwa Aure Baza'a Dai Na Shiba Sannan Kuma Haka Itama Soyayya Baza'a Dai Na Taba.


To Idan Mawaki Ya Rike Wannan Salon Guda Biyu Ina Mai Tabbatar Dacewa Zai Samu Daukaka Sosai Toh Abunda Yadaga Darajar Wadancan Mawakan Guda Biyu Kenan Wanda Mukayi Bayaninsu A Sama Nura M Inuwa Da Umar M Shareef .


To Bincike Ya nuna Yanzu Mawaki Hamisu Breaker Shine Wanda Tauraruwarsa Take Haskawa Kuma Duniya Takeyi Dashu A Yanzu Munaso Idan Kai Mawakin Hamisu Breaker Ne Ka Ajiye Mana Sunan Wakar Datafi Burgeka Acikin Wakokin Dayayi.

SHARE

Author: verified_user

0 Comments: