Idan Baku Manta Ba Akwanakin Baya Ranar 10 Ga Watan Maris Fitaccen Jarumin Kannywood Wato Ali Nuhu Yake Murnar Cikarsa Shekara 47 A Duniya.
Yadda Har Mukaga Yan Uwa Da Abokanan Aiki Wato Yan Masana'anatar Kannywood Din Mazansu Da Mata Suke Tayashi Murna Ta Hanyar Wallafa Hotunansa A Shafukansu Na Sada Zumunta Daga Facebook Zuwa Instagram.
Duk Da Dai A Zamaninmu Na Yanzu Da Kuka Sani Ba Sai Akan Jarumai Ba Har Ma Da Samari Da Yam Mata Zuwa Kananan Yara Wannan Abun Tana Kasancewa Dasu Yadda Muke Ganin Ana Wallafa Hotunan Mutanen Dasuke Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsu Wadda Muke Kira A Turance Da Birthday.
Hakan Ne Ta Faru Ga Jarumi Ali nuhu Yadda Muka Ga Abokan Aikinsa Suna Wallafa Hotunansa Tare Da Tayashi Murna Da Kuma Fatan Samun Shekaru Na Gaba Masu Karko Da Albarka Kamar Yadda Akeyi A Zamani Yanzu Wasu Ma Har Sukan Wallafa Wasu Hotuna Cikin Bidiyo Hade Da Waka Domin Taya Jarumin Murnanr Wannan Rana Ta Farin Cikinsa.
Toh Kamar Yadda Muka Fada Muku masana'antar Kannywood Ta Kunshi Mutane Da Dama Kama Daga Yam Mata Da Samari Hade da Manyan Mutane, Kamar Yadda Kuka Sani A Rayuwa Dai Yanzu Wani Sai Da Wani Ma'anar Wannan Kalami Namu Shine Ta Sanadiyyar Wani Allah Yake Daga Wani Koh Ba Haka Bane.
Toh Kamar Haka Ma A Masana'antar Kannywood Din Take Wasu Suna Yin Silar Tasowar Wasu Har A Sansu a duniya Domin ita Daukaka Ta Duniya Tana Zuwane Da Sila, Kamar Yadda Kuka Sani A Duniyar Fina-finan Hausa Jarumi Ali Nuhu Yana Daya Daga Cikin Jaruman Da Tauraruwarsu Take Haskawa Har Kuma Wasu Su Haskaka Ta Sanadiyyarsa Domin Irin Daukakar Da Allah Yayi Masa A Masana'antar.
Domin Kuwa Tun Farkon Fitowar Jaruma Rahama Sadau Cikin Masana'antar Tashigo Ne Ta Sanadiyyar Jarumi Ali Nuhu Wanda Yakeyin Fina-finansa Da Ita Har ma Da Wasu Bidiyoyin Wakokin Hausa Da Ake Aiwatarwa, Toh Ta Haka Jarumar Tayi Suna Sannan Kuma Ta Samu Daukaka Da Masoya.
Baya Da Haka Shima Jarumi Sadik Sani Sadik Yayi Tashe Ne Ta Silar Jarumi Ali Nuhu Yadda Ya Zamto Yayi Silar Daukakarsa Yadda Sukeyin Film Tare da Sauran Abubuwa Wanda Akeyi Da Zai Daga Darajar Jarumi idan Farkon Shigowane Acikin Masana'antar.
Baya Da Wadannan Har Da Yarinyar Nan Wato Maryam Yahaya Itama Ta Silar jarumi Ali Nuhu Allah Yabata Daukaka Da Kuma Masoya Yadda Har Sai Da Tazamto Jaruma Mai Tashe A Masana'antar Kuma ana Damawa Da Ita Akoda Yaushe Har Zuwa Yanzu, Jaruman Da Ali Nuhu Yayi Silar Tashinsu Da Kuma Samun Masoyansu Suna Da Yawa Sosai Acikin kannywood.
Idan Zaku Iya Tunawa Dai Muna Kan Batunmu Da Bikin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Ali Nuhu , Duk Da Kun San Jaruman da Mukayi Bayani Akansu A Sama Rahama Sadau Da Sadik Sani Sadik, Idan Baku Manta Ba A Kwanakin Baya Rahama sadau Tayi Wani Abu Wanda Ya Janyo Mata Zagi Da Mabiyanta Har ma Da Abokan Aikinta Acikin Masan'antar Yadda Har Wannan Gangami Na Yi Mata Korafi Yahada Harda Jarumi Ali Nuhu Da Adam A Zango.
Baya Da Haka Sai Muka Ga Jarumar Ta Daina Bibiyar A Shafukan Sada Zumunta Bisa Ga Dubawa Munsan Jaruman Kannywood Alakarsu Tafi Karfi Musamman A Shafin Instagram Toh Sai Muka Ga Sun Daina Bin Juna Daga Rahama Sadau Zuwa Ali Nuhu Ma'ana Sun Yanke Alakarsu Ta Kafafen Sada Zumunta.
Toh A Lokacin Da Ali Nuhu Yake Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa Rahama Sadau Bata wallafa Hotonsa Ba Domin Tayashi Murnar Hakan Sai Mukaga Tayi Biris Da Abun Sabanin Ba Haka Suka Saba Yiba A Kwanakin Baya Kafin Wanann Abun Yafaru.
Shima Haka Jarumi Sadik Sani Sadik Munga Bai Wallafa Hoton Ali Nuhu Ba Lokacin Da Yake Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa, kamar Yadda A Kwanakin Baya Muka Ga shima Sadik Sani Sadik Din Yayi Bikin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa Amma Bamu Ga Jarumi Ali Nuhu Ya Wallafa Hotonsa ba Domin Tayashi Murnar Haka.
Abun Dai Yasamo Asaline A Wata Doguwar Hira Da Akayi Da Sadik Sani Sadik Din Da Gidan BBC Hausa Lokacin Dasukayi Masa Wata Tambaya Akan Cewa Wayene Ubangidanka A Kannywood Yanzu? Sai Jarumin Ya Kada Baki Yace Shi Yanzu Bashi Da Wani Ubangida Sai Kadai Yake Gudanar Da Harkokinsa, To Abunda Muke Zaton Hakane Yahadasu Da Ali Nuhu Tunda A Sama Munyi Bayani Akan Ali Nuhu Shine Silar Dagowarsa A Masana'antar.
Toh Allah Ya Kyauta Mungode Da Sauraran wannan Shiri Sannan Kuma Mungode Da Kasancewa Damu Dakukayi.
0 Comments: