Saturday, March 27, 2021

Gaskiyar Lamari Game Da Makancewar Jarumin Kannywood Alhaji Shehu Hassan Kano

SHARE

 


Fittaccen Jarumi Kuma Wanda Ya Zamto Jigo A Masana'antar Kannywood Wato Alhaji Shehu Hassan Kano Ya Musanta Rade-Radin Da Akeyi Akansa Nacewa Ya Makance.


Kamar Yadda Kuka Sani A Rayuwar Yanzu Musamman A Kafafen Sada Zumunta Wasu Lokutan Ana Samun Karairayi Ana Alakantasu Ga Jarumai Musamman Yan Shirin Film Din Hausa, Ko Karyayr Mutuwa Ko Kuma Ta Rashin Lafiya.


Idan Zaku Iya Tunawa Kamar Wata Tsohuwar Jarumar Masana'antar Kannywood Wato Fati Bararoji An Taba Danganta Mata Wata Karya Akan Cewa Ta Mutu, Baya Da Haka Kuma A Jiya Ma Muka Samu Labarin Jamila Nagudu Ma Anacewa Ta Mutu , Sannan A Kwanakin Baya Wannan Karyar Antaba Dangantata Ga Fitacciyar Jarumar Nan Wato Hadiza Gabon.


Toh Wannna Bashine Karo Na Farko Da Akeyiwa Jaruman Kannywood Wadannan Karairayi Ba Domin Shima Shehu Hassan Kano Din Yaji Ana Cewa Ya Makance Ma'ana Ya Zama Makaho, Shine Sai Yayi Wata Hira Da Dokin Karfe Yadda Yake Bayyana Musu Cewa Sakamakon Ba'a Ganinsa Acikin Fina-finan Hausa Yanzu Ba Komai Bane Saboda Anyi Masa Gyaran Ido Ne.


To Sai Yan Jarida Suka Sake Tambayarsa Akan Cewa Sunji Ana Cewa Ya Makance Toh Yayi Bayani da Bakinsa Domin Ya Fitar Da Mutane Daga Rudani Da Kuma Cece-kuce, Daga Nan Jarumin Yayi Bayani Dacewa Ai Ita Rashin Lafiya Babu Wanda Ya Tsallaketa Sannan Kuma Idan Kaddararka Ce Baka Isa Ta Wuce Kaba Sai Ta Sameka Yakamata Mutane Munayiwa Kanmu Adalichi Acikin Zance Ba Muna Daukan Zancen Dabashi Da Tushe Ana Yadawa A Kafafen Sada Zumunta.


Sannna Baya Da Haka Shehu Hassan Yaci Gaba Dacewa Ina Mai Bawa Masoyansa Hakuri Da Nan Bada Jimawa Ba Zai Dawo Bakin Aiki A Dora Kamar Yadda Aka Saba Akoda Yaushe Sannan Yana Bukatar idan Wannan Sako Ya Riskeka Ka Watsa Zuwa Wani Wajen Domin Yaje Kunnen Wadanda Basuji wannan Bayaninba.


Toh Nima Bari Na Danyi Mana Tsokaci Yakamata Mutane Mugane Cewa Duk Abunda Ka Fada Fa Game Da Wani Idan Ba Dai - dai Bane Takan Iya Yiwuwa kadauki Hakkinsa Domin Kuwa watakila A Wannan Abunda Zaka Ce Ka Iya Cutar Dashi Ko Kuma Ka Janyo Masa Bakin Jini Awajen Wasu.


Basai Mutum Yayi Jinya Ba Ko Mutuwa Akwai Karya sosai Da Ake Dangantata Ga Jarumai kai Ko Ba Jarumai Bama Da Sauran Mutane Na Gari Yakamata Ana Tsaya Ana Tabbatar Da Zance Kafin A fitar Dashi Idan Zai Amfani Jama'a Idan kuma Bazai Amfana Bama Kawai Barinsa Yafi Amfani Toh Ya Kamata Mutane Mu Gane Gaskiya Dan Allah Shinenan Allah Yasa Mudace Ameen.



SHARE

Author: verified_user

0 Comments: