Thursday, March 25, 2021

Mutuwar Sayyada Rabi'atu Haruna Ta Gigiza Jama'an An Bayyana Dalilin Mutuwarta

SHARE

 


Fitacciyar Mai Wakar Begen Annabi Muhammad (S A W) Sayyada Rabi'atu Haruna Allah Yayi Mata Rasuwa.

Kamar Yadda Kuka San Wannan Matar Wato Sayyada Rabi'atu Haruna Ta Kasance Tana Yin Wakar Begen Annabi Muhammad (SAW) A Garin Kano Yadda Takasance Akoda Yaushe Tanayin Wakar Begen Cikin Hikima Da Ku.a Fasaha.

A Maganar Gaskiya Sayyada Rabi'atu Tana Daya Daga Cikin Mawakan Mata Wanda Suka Kware Wajen Wakar Bege, Baya Da Haka Ta Samu Dubunnan Masoya A Arewacin Nigeria Harma Sa Wani Bangare Na Kudanchi , 

Sayyada Rabiatu Dai Bata Tsaya Anan Ba Har Ma Da wasu Wakokin Tanayi Wanda Suka Danganchi Bege ne Da sauransu, Toh Kawai Muna Tsaka Dajin Dadin Wakokin Bege Da Ta Keyi Na Manzon Tsira Domin Duk Wanda Yake Sonsa Muma Muna Sonsa.

A Yau Kuma Sai Muka Tashi Da Wani Al'amari Marar Dadi Game Da Ita Amma Duk Da Haka Muna Yi Mata Fatan Alkhairi Da Allah Ya Jikanta Abun Ba Komai Bane Face Allah Yayi Mata Rasuwa, 

Bayan Mutuwar Sayyada Rabi'atu Haruna Anyi Wata Hira Da Mijjnta Yadda Ya Bayyana Silar Rasuwar Matar , Acikin Hirar Dai Mijin nata Yake Cewa A Gabannin Mutuwar Ta Tayi Rashin Lafiya Sosai Daga Baya Allah Ya Karbi Abarsa.

Baya Da Haka BBC Hausa Ta Tambayi Mijin Nata Akan Yaya Al'amarin Zaman Aurensu Yakasance Lokacin Tana Raye Take Wannan Harkar Waka Ta Bege? Mijin Nata Ya Kada Baki Yace eh A Gaskiya Lokacin Da Mukayi Aure Da Ita Dama Nasan Tana Harkar Wakar Bege Kuma Na Barta Taci Gaba Da Wannan Harka Duk Da Akwai Igiyar Aurena Akanta.

Baya Da Haka Nasan Ba Wata Harka Take Ta Waka Wanda Addini Bai Yadda Da Ita Ba Harka Ce Ta Yabo Na Annabi Muhammad (SAW) Kuma Nima Masoyinsa Ne Shiyasa Na Barta Taci Gaba Da Wannan Harkar Kuma Ina Bata Kwarin Guiwa Akan Haka.

Sannan Yace Wani Lokaci Mutane suna Yimin Magana Akan Haka Ni Kuwa Ina Fada Masu Akan Waannan ai Ba Komai Bane Tunda Harka Ce Ta Yabon Manzon Allah, Sannan Kuma A Kullum Ina Mai Jin Dadin Haka Saboda Wannan Ba Karamin Abu Bane Ace Matarka Tana Da Baiwar Yin Begen Annabin Tsira.

Baya Da Haka Yakara Dacewa Duk Da Mutuwa Dole Ce Kuma Gaskiyace Akan Kowa Amma Nayi Bakin Cikin Rabuwa Da Ita Domin Kuwa Ban Taba Rasa Wata Kulawa Daga Gareta Ba.

Daga Karshe Ina Mai Nema Mata Tsira Daga Allah Sannan da Kuma Addu'ar Allah Ya Jikanta Da Rahama Ameen.

Toh Jama'a Kunji Yadda Hirar Nan Takasance Tsakanin Mijin Sayyada Rabi'atu Haruna Bayan Mutuwarta Zamu so Mukarbi Ra'ayoyinku Game Da Jana'izar Mutuwarta.

Daga Karshe Muma Muna Yi Mata Fatan Alkhairi Da Allah Ya Gafarta Mata Ya Kuma Jikanta Da Rahama Mukuma Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu cika Da Imani Ameen.

SHARE

Author: verified_user

0 Comments: