Thursday, March 25, 2021

Tirkashi Asirin Wata Budurwa Ya Tonu Yadda Ta Kashe Saurayinta Har Lahira

SHARE

 


A Yau Kuma Sai Muka Tashi Da Wani Sabon Labari Marar Dadi Yadda Wata Budurw tayi Sanadiyyar Kashewa Tsohon Saurayinta Ta Hanyar Yin Garkuwa Dashi.

Rundunar Yan sandan Jihar SokotoTayi Nasarar Cafke Wata Budurwa Ita Da Saurayinta Da Kuma Wasu Mutane A Kalla Guda Biyar Da Ake ZarGinsu Da Kisan Gilla Akan Wani Mutumi Ta Hanyar Yin Garkuwa Dashi, 

Lamarin Dai Ya Tada Hankulan Jama'a Sosai Yadda Akayi Mamakin Yadda Wannan Al'amari Ya Auku Amma Duba Da Yanayin Juyin Zamani Wanann Bai Zamam Komai Ba Domin Ana Samun Misalin Irin Wadannan Abubuwa Kullum Kuma Basau Daya Ko Sau Biyu Ba Sai Dai Muce Allah Ya Kyauta .

Abba Abbey Wanda Mataimakine Ga Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Kuna Dan Majalissa Mai Wakiltar Sokoto Ta Tsakiya Ta Aliyu Magatakarda Wamako, Ya Gamu Da Ajalinsa ne Tasanadiyyar Tsohuwar Budurwarsa Wadda Ta Hada Baki Da Wani Sabon Saurayinta Da Kuma Ragowar Wasu Mutane Akalla Guda Biyar Wajen Yi Masa Kisan Gilla.

Lamarin Yafaru Ne A Ranar Alhamis Da Dare Wanda Ana Washegarin Juma'a Abba Abbey Yace Ga Garinku Nan,  Amma Kuma Zamu Bayyana Muku Silar Faruwan Hakan Tunda Akwai Alamun Tambaya Akan Wanann Al'amari.

Wasu Majiyoyi Sun Bayyana Mana Cewa Ana Zargin Tsohuwar Budurwar Marigayin Hade Da Sabon Saurayinta Da Kuma Wasu Mutane Yadda Sukayi Masa Kisan Gilla Sanann kuma Suka Jefar Da Gawar Akan Titin kihar Sokoto Dake Yankin Garin Durbawa Karamar Hukumar Mulkin Kware A Jihar Sokoto.

A Cewar Wata Majiya Kusa Damu Budurwar Mai Suna Fatima Bintu Riskuwa Tana Soyayya Ne Da Abba Abbey  Yadda Har Lamarin Yakai Gayin Zancen Aure Daga Baya Kuma Suka Samu Matsala Yadda Har Maganar Auren Ta Lalace Sai Fatima Ta Yi Wani Sabon Saurayin Mai Suna Umar Abubakar.

Haka Zalika Fatima Da Umar Sunyi Kudurin Yin Aure Toh Sai Kuma Mtsla Tashigo Musu Ta Rashin Kudi, Shind Fatima Taje Wajen Saurayinnata Wato Abba Abbey Kenan Marigayin Tace Ya Taimk Mata Da Kudi Zatayi Aure A Cewar Majiyar Data Kawo Mana Labarin.

Shine Sai Fatima Ta Shirya da Sabon Saurayin Nata Umar Akan Suje Su Sace Abba Abbey Sannan Su Nemi Kudin Fansa Idan Aka Basu Sai Suyi Aure Da Kudin, To Yadda Hakarsu Bata Cimma Ruwaba Kenan Har Sukayi Sanadin Kashe Wanda Sukayi Garkuwa Dashi Din Wato Abba Abbey.

Majiyar Ta Ci Gaba Da Cewa Fatima Ta Shirya Ta Kira Shi Tsohon Saurayin Nata Wato Abba Abbey Inda Tace Masa Tana Wani Shago Na Siyarwa Kayayyaki Tace Yazo Yakaita Gida A Motarsa, Dayajeshi Wajen Sai Ya Ganta Tare Da Wani Yadda Ta Bayyan Masa Cewa Dan Uwanta Ne Sukace Ya Mikasu Wata Unguwa Daya Kaisu Sai Da Sukaje Wani Loko Ma'ana lungu Yana Kokarin Fitowa Sai Yaga Wata Motar Ta Rufeshi Ta Baya Sannan Yaga Wasu Mutane Sun Fito Da Wata Bindiga Kirar Ak - 47 Sai Suka Kamashi Abba Abbey Din Ma'ana Sukayi Garkuwa Dashi.

To Sai Dai Kafinnan Rohotannin Sun Bayyana Cewar Abba Abbey Yayi Kiran Abokansa Da Suke Hulda Dasu Akan Su Ranta Masa Kudi Saboda Anyi Garkuwa Dashi Ya Kira Mutane Dayawa Daga Baya Kuma Kudurinsa Bai Samu Cikaba , 

Wannan Lamarin Ya Auku Ne Bayan Wadanda Sukayi Garkuwa Dashi Din Sun tabbatar Dacewa Bashi Da Kudi Sanann Kuna Sun Duba Asusunsa Na Banki Ta Wayar Salularsa Basi Ga Wani Kudi Ba shiyasa Sukace Toh Ya Nemo Musu Kudi Ko Kuma Su Kashe Shi Lamarin Dayasa Ya Kasa Samun Kudin Ko Da Kuwa Daga Wajen Abokan Harkara.

Hakan Ne Yabawa Wadanda Sukayi Garkuwa Dashi Din Damar Kashe Shi Ta Hanyar Karya Gabobin Jikinsa Tare Da Takashi Da Motar Dasuka Dauko Shi Da Ita.

To Sai Dai Hausawa Suna Cewa Rana Dubu Ta Barawo Ce Rana Daya Kuma Ta Mai Kaya Ce Domin komai Abunda Mutum Yakeyi Allah Yana Ganinsa Kuma Wani Lokaci Zai Yi Dana Sanin Aikata Wannan Laifi Baya Da Haka Da Wadannan Mutane Sukayi Nasarar Kashewa Shi Wanann Marigayin Sai Suka Daukeshi Suka Kai Shi Bakin Titi Suka Jefar Dashi A Washe Garin Jumma'a Mutane Suka Ganshi Aka Kaishi Asibiti Domin A Duba Lafiyarsa Amma Haka Bata Cimma Ruwaba Kafin Aje Asibiti Ya Mutu.

Yadda Asirin Wadannan Mutane Ya Tonu Shine Angano Sunan Fatima Ne ta Wayarta Yadda Aka Ga Abba Abbey Shine Mutum Na Karshe Data Kira Sannan Kuma Da Taimkon Allah Wajen Bayyana Mugayen Mutane Yadda Aka Kamata Ka Kaita Kotu Take Bayyana Abunda Ya Faru Tsakaninsu,

Sannan Kuma A Wajen Karbar Abba Abbey Din Anyi Wata Musayar Wuta da Wadanda Suka Daukeshi Din Da kuma Yan Sanda Yanda Dasuka Ga Abun Babu Dama Suka Kasshehi Toh Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa mu Kuma Allah Ya Rabamu Da Sharrin Zuciya Ameen.

Muna So Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Lungu Da SakoNa Fadin Kasar Nan har Ma Da Wasu Kasashen Domin Yazama iznah Ga Yan Baya Sai Dai Muce Allah Ya Kyauta.



SHARE

Author: verified_user

0 Comments: