Assalamau Alaikum Jama'a Barkanmu Da Warhaka Sannunmu Da Sake Saduwa A wani Sabon Shiri,
Kamar Yadda Kuka Sani Aure Sunnah Ce Ta Annabi Kuma Allah Ya Umarcemu Da Mu Aiwatar Dashi Idan Da Damar Yin Hakan.
Toh A Yau Kuma Sai Muka Tabo Wani Bangare Na Ma'aurata Yadda Zamuyi Bayani Tare Da Taimko Na Wadanda Suke Fama Da Wannan Cuta Kamar Yadda Kuka San A Yanzu Cututtuka Sunyi Yawa Wadanda Muka Sani Da Wadanda Bamu Sani Ba, Sannan Da Wadanda Suke Damunmu Da Kuma Wadanda Suke Jikinmu Bamu Sani Ba.
Toh A Yau Insha Allah Zamu Bayyana Wasu Cututtuka Dasuke Addabarmu A Yanzu Musamman Wannan Cuta Ta Sanyi Da Take Damun Ma'aurata A Wajen Jima'i, Kamar Yadda Kuka Sani Wasu Lokutan Ana Samun Cutar Da Take Damun Mutane Musamman Ma'aurata.
Toh Kunsan Dai Cutar Sanyi Wata Muguwar Cutace Da Idan Takama Mutum Idan Baiyi Da Gaske Ba Takan Iya Bashi Matsala Game Da Lafiyarsa Sannan Tana Kawowa Rashin Kuzari Wajen Saduwa, Shi Wanann Lakani Dazamu Bayar Daga Maza Har Mata Zasu Iya Amfani Dashi Sannan Kuma Koda Bakada Aure Kana Iya Amfani Dashi Domin Zai Taimaka Maka Kwarai Wajen Lafiyarka.
Domin Duk Daren Dadewa Zakayi Auren Sanann Kuma Ko Babu Aure Yanzu Bakasan Ta Wacce Hanya Cutar Sanyi Zata Kamaka Ba Da Farko Zamu Kawo Muku Abubuwa Guda Hudu Masu Sauki Wanda kuma Muke Bukatar Ku Mallakesu A Yayin Hada Wannan Magani ,
Da Farko Da Abubuwan Ba Wasu Abubuwa Bane Masu Wahalar Samu Da Har Mutum Zai Iya Tsorata Ko Wani Abu Game Da Haka Ita Cuta Da Kuke Ganinta Duk Girmanta Toh Sai Kaga Maganinta Bashi Da Wahalar Samu Dai Sai Kasala Ko Sakachi Na Mutane.
Toh Dafarko Dai Kada Mucikaku Da Surutu Ga Abubuwan Nan Zamu Zayyana Muku A Kasa Tare Da Cikakken Bayaninsu;
(1) Namijin Goro
(2) Citta Mai Yatsu
(3) Lemon Tsami
(4) Tafarnuwa
Bari Muyi Bayani Akan Namijin Goro Da Farko Da Kunsan Namijin Goro Wani Dan itaciya Ne Dayake Da Mutakar Al'ajabi Da Kuma Amfani Musamman Bangaren Maganin Cututtuka Da Dama.
Muna So Kasamu Namijin Goro Ka Dakashi Zuwa kamar Gari Haka Ma'ana Kasamu Abunda Zaka Dakashi Yazamto Kamar Gari-gari Haka sannan Kuma Yazamto Ya Bushe Domin Zai Iyayin Wahala Idan Yamana Yana Danyensa Zaka Dakashi To Ka Bari Ya Bushe Sai Ka Dakashi Yazama Garinsa Haka,
Bayan Ka Daka Namijin Goro Sai Ka Samo Citta mai Yatsu Kamar Yadda Mukayi Bayani A Sama, Wato Ita Citta Mai Yatsu Tasha Bam-bam Da Citta Da Muke Amfani Da Ita Wajen Yin Shayi Ko Kuma lemo Haka Da Dai Suransu Domin Ita Citta Mai Yastu Ma Amfi Samunta A Danya Ba'a Fiye Samunta A Bushe Ba Sabanin Cittar Da Muke Amfani Da ita A Bushe Take,
To Sai Ka Nemo Citta Mai Yastu Dinka Idan Kuma Baka Santa Ba Kaje Ka Kasuwa Wajen Masu Sayar Da Kayan Kamshi Ka Tambaya Kace Kana son Abaka Citta Mai Yastu Zasu Baka Toh Idan Kasameta Zaka Dakata Itama Ko Bata Zama Garri Ba Ka Dakata Kamar Yadda Ka Daka Namijin Goron Naka Idan Ka Dakasu Sai Kazo Ka Hada Su Waje Daya A Tukunya ka Zuba.
Baya Da Haka Sai Ka Dauko Tafarnuwarka Kamar Tadda Kuka San Tafarnuwa Dai Basai Nayi Bayani Ba Domin Idan Ba Tafarnuwa Ba Bansan Wani suna Kuma Da Ake Kiranta Ba Koma Bayan Wannan Sai dai Ba Yaren Bahaushe Ba, Idan Kasamota Itama Kasamo Bushasshiya Domin Yawanci Ma Anfi Samun Tafarnuwa A Bushe Ba'afiye Samun Danya Ba.
Toh Idan Ka Samota Sai Kazo Itama Ka Dakata Idan Ka Dakata Sosai Tazama Kamar Garri Kamar Yadda Kayiwa Namijin Goro sai Ka Zubata Acikin Tukunyar Daka Zuba Citta Mai Yatsu Da Namijin Goro Itama Ka Zuba Garrinta Ka Hadasu Amma Fa Kada Ka Yarda Da Cewa Bazaka Daka Da Kanka Ka ba Ma'anaa Ko Zaka Iya Zaton A Kwai Wanda A Dake Yake A Kasuwa Bari Kaje Ka Siyo Kazo Ka Hada Gaskiya Wannan Ba Lallai Yayi Maka Aiki Kamar Yadda Zakayi Komai Da Kanka Ba.
Bayanka Zuba Wadannan Abubuwa Guda Uku Acikin Tukunya Toh Sai Ka Samo Lemon Tsami Shima Ka Tatse Ruwansa Mai Yawa Acikin Tukunyar Dauke Da Dakakkun Kayan Nan Namijin Goro citta Mai Yatsu Da Tafarnuwa, Sai Ka Zuba Ruwa Dan Kadan Sai Ka Kunna wuta Har Wannan Abun Ya Tafasa Idan Ya Tafasa sai Ka Daukoshi Ka Tace Ruwan A Kwano Ko Kofi Sannan Sai Ka Nemo Zuma Ka Zuba Acikin Ruwan Ka Hada Kana Sha Kullum Da Safe Kafin Komai Yahe Cikinka In Allah Ya Yarda Zakaga Chanji Sosai Da Sosai A Rayuwarka .
Munaso Ku Watsa Wannan Bayani Namu Domin saura Su Amfana Mungode.
0 Comments: