Thursday, March 25, 2021

Yadda Ado Gwanja Yasha Zagi Daga Mabiyansa Akan Wani Abu Daya Aikata

SHARE

 


Fitaccen Mawaki Kuma jarumi A Masana'antar Kannywood Wato Ado Gwanja Yasha Zagi Da Bakaken Kalamai Daga Mabiyansa Akan Abunda Ya Aikata.

Wadda A Watanin Dasuka Wuce Ne Muka ga Ya Wallafa Wasu Hotunansa Tare Da Wasu Yam Mata Da Shigar Damammun Kaya Matan Dai Kana Ganinsu Sunyi Kama Da Yan Kudu, Saboda Suna Sanye Da Kaya Babu Hijabi Sai Ma Wasu Na Sanye Da Mawafi, 

Jarumin Dai Ya Wallafa Wannan Hotunan Sannan Yace ; Duk Wani Mai Abun Fadi Toh Ga Dama Tasamu ! A Lokacin Sai Mutane Sukayi Ta Mayar Masa Martani Kamar Yadda Ya Bukata, Idan Zaku Iya Tunawa A Kwanakin Baya Wani Malami Ya Fito Yace Da Ado Gwanja Da Mawaki Hamisu Breaker Suna Kan Gaba Wajen Lalata Tarbiyar Yaran Hausawa, 

A Lokacin Da Malamin Yasaki Wannan Tsokaci Mutane Da Dama Basu Yarda Da Maganar Wannan Malamin Ba Sai Kuma Wasu Sun Soki Ra'ayin Wannan Magana Tasa Ganin Cewa Ba'a Taba Samun Aibu Na Mawakan Guda Biyu Ado Gwanja Da Hamisu Breaker Dinba, 

To Sai Kuma Yanzu Muka Ga Ado Gwanja Yana Nuna Wasu Alamu Na Kishin-kishin Din Gaskiyar Abunda Malamin Yafada Duk Da Haka Mutane Da Dama Sunyiwa Ado Gwanja Martani Sosai Marasa Dadi Kamar Yadda Ya Bukata , 

Ga Kadan Daga Cikin Mutanen Dasukayiwa Ado Gwanja Martani Akan Wadannan Hotuna:

Farouk Kbr- Yace Haba Liman Tunda Kace Sama Mata Har Yau Baka Sakko Ba 

Hali Dubu - Yace Toh Dubi Sai Malam Ya Fito Yana Magana Kuzo Ku Nayi Masa Raddi 

Official Solly - Yace Dama Da Matarka Kake Irin Wannan Amma Gaskiya Na Tausaya Mata Idan Taga Haka 

Musa Ai - Yace Kai Ina Rabaka Da Kiwon Kyalli Kana Cewa Kyalli Ta Haihu Koh Da Bahaushe Nake.

Wadannan Sune Kadan Daga Cikin Kalamai Kala-kala Da Mutane Sukayi Tayiwa Ado Gwanja A Shafunsa Na Instagram Akan Wannan Hoto Daya Wallafa Yana Tsakiyar Yam Mata Da Shigar Damammun Kaya, 

Toh Bayan Wucewar Wannann Al'amari Kuma Sai Muke Bibiyar Jarumin A Shafukansa Na Sada Zumunta Sai Muka Ga Ya wallafa Wani Hoto Acikin Bandaki A lokacin Daya Wallafa Wannan Hoto Munga Yasakashi Da Bakar Filter Yadda Tayi Duhu-duhu Sannan Yace Alhamdulillah A Kasan Hoton, 

Toh Duk Da Ba Wani Abu Yayi Ba Wanda Zai Daga Hankalin Mutane Sai dai Kasan Al'amari Na Yan Masana'antar Kannywood Dasukeyi Game Da Rayuwarsu Ko Kuma Wani Abu Yana Janyo Cece-kuce Sosai Musammman Ma A Kafafen Sada Labarai.

Toh Kamar Hakan Ne Yafaru Ga Jarumin Yadda Ya Wallafa Wannan Hoto A Lokacin Sai Mutane Sukayi Tayi Masa Munanan Kalamai Wasu Suna Nuna Rashin Jin Dadin Ganin Wannan Hoto Duk Da Shi Wannan Hoto Da Ado Gwanja Ya Wallafa Ba'a Cikin Babdakin Gargajiya Ya Wallafashi Ba Acikin Bandakin Zamani Ne Dauke Da Ado Kala-kala Acikin Amma Duk Da Haka Wasu Daga Cikin Mabiyansa Basuyi Kasa Aguiwa Ba Wajen Nuna Fushinsu Game da Wannan Hoto Mutanen Dasuka Yiwa Ado Gwanja Akan Wannan Hoto Sune:

Iserh Yace - Haba Abokina Hoto Acikin Toilet Ado Gwanja A Koma Islamiyya, 

Habiba Usy Tace - Hotonma Sai Anyi Acikin Toilet Wajen Kazanta Saboda Tsabar Kazantar Wajen Akace Mana Sai Munyi Addu'a Kafin Mu Shigeshi Gashi Kai Kuma kazo Kana Yin Hoto Aciki Gaskiya Yakamata Ka shiga Islamiyya.

Sarki Fan Yace - Haba Ado Gwanja Wannan Ai Sai Ka Bayar Damu Mu Mutane Kano Haba Hoto Acikin Bandaki Wallahi Wannan Kayi Kama Da Mutane Zaria 

Queen Aisha Tace - Ban Taba Gani Anyi Hoto Acikin Bandaki Ba Sai Akanka Gaskiya Kana Bamu Kunya .

Usman a Isah Yace - Kashinma Baza'ayi Acikin Salama Ba Sai An Nunawa Duniya Toh Wannan Sai Dai Muyi Maka Addu'ar Shiriya Allah Ya Kyauta.

Wannan Sune Kadan Daga Cikin Kalamai Kala-kala Da Mutane Sunayi Tayiwa Ado Gwanja Akan Wadannan Abubuwa Dayake Sakawa A Shafinsa Na Sada Zumunta Musamman A Instagram Da Facebook.

Sai Ku Kasance Damu Domin Samun Labaran Kannywood  A Koda Yaushe Muna Bukatar Ra'ayoyinku Game Da Wannan Bayani Mungode Da Kulawarku.

SHARE

Author: verified_user

0 Comments: